Aikin noma a Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya damu matuka da tsadar kayan abinci kuma ya kuduri aniyar samar da abinci a farashi mai sauki, in ji ministan yada labaran sa.
Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta karbo aron ¥15bn daga wata hukumar ƙasaar waje domin bunkasa harkar noma a Najeriya, sai an shekara 30 ba a gama biya ba.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana irin matakan da ya soma ɗauka bayan samun bayanan ana shirin kai hare-hare makarantu da gonaki a Osun.
Majalisar wakilai ta ce rashin tsaro da aka dade ana fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya ya jawo karancin samar da abinci a kasar.
An gano fasa kwauri da ambaliya a matsayin musabbabin karancin abinci da tsadar rayuwa. Wannan dai na fitowa daga gwamnatin Najeriya ta bakin ministan noma.
Mun kawo labarin inda aka kwana game da alkawarin raba kayan abinci saboda ana yunwa. An tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa talakawa.
Tun kwanakin baya gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a fito da buhunan hatsi a raba. An shafe makonni 2 da yin alkawarin rabon hatsi, ‘yan Najeriya suna jiran tsammani.
Ministan tattalin arzikin kasa, Olawale Edun ya ce farashin abinci zai fado. Gwamnatin tarayya za ta raba buhuna 1, 407,205 domin farashin abinci ya sauko.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi jan-kunne a game da hadarin bude iyakoki a shigo da abinci. Tinubu ya ki daukar shawarar Kashim Shettima a kan kayyade farashin abinci
Aikin noma a Najeriya
Samu kari