Kudu maso gabashin Najeriya
Gwamna Fubara ya bada umarni cewa shugabannin kananan hukumomi su mika mulki, yayin da Kotun Koli ta hana Ribas samun kudaden gwamnati daga CBN da Akanta Janar.
Makinde ya jajanta wa iyalan Sarkin Sasa, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Hausa/Fulani, ya kuma yi masa addu’ar samun Aljanna Firdausi.
Kungiyar Afenifere ta bukaci kariyar gaggawa ga Farfesa Adeyeye, tana mai cewa barazana a kanta barazana ce ga lafiyar al’umma da tsaron kasa baki daya.
Rundunar 'yan sanda ta kama wani Gbolahan Adebayo bisa zargin kashe budurwarsa da duka a Legas. An dauki gawarta zuwa asibiti domin gudanar da bincike.
Rikicin kabilanci tsakanin mazauna garuruwan Gbelemonti da Maidoti a jihar Edo ya jawo mutuwar mutane 7, tare da jikkata 6. ‘Yan sanda da sojoji sun dakile lamarin.
'Yan bindiga sun harbi fasto tare da sace mutum 6 a wata cocin jihar Delta. Masu garkuwa ba su tuntubi kowa ba, amma jami’an tsaro na kokarin ceto su.
Jam'iyyar LP na ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da PDP, ciki har da Valentine Ozigbo, dan takarar gwamna, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a Anambra.
PDP ta fara sayar da fom ɗin takarar gwamnan Anambra, zaɓen fidda gwani zai gudana 5 ga Afrilu, yayin da za a mika sunan ɗan takara zuwa ga INEC a ranar 22 ga Mayu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya jajanta bayan rasuwar shugaba a kungiyar PANDEF, Cif Edwin Clark a yau Talata inda ya ce an yi rashin kishin kasa.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari