Bikin Sallah
Rundunar ‘yan sandan Kano ta musanta karbar wasikar sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero kan neman tsaro domin gabatar da bikin hawan sallah babba.
Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautar jihar Kano, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawan babbar sallah kamar sallah har ya gayyaci hakimai.
Barayi sun haura har gida tsakar rana sun sace ragon layya a birnin tarayya Abuja. Barayin sun shiga gidan ne tsakar rana yayin da mutumin ya fita.
Tsadar abinci na kokarin hana mutane sayan ragunan sallah a birnin Jalingo da ke jihar Taraba. Dillalan raguna sun koka kan rashin kasuwa duk da kokarin da suke.
Bayan Sanata Abdulaziz Yari ya raba ragunan, Hon. Aminu Jaji shi ma ya ba ƴan mazaba raguna 300 da makudan kudi har N250m ga shugabannin APC da mambobinsu.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da biyan albashin ma'aikata na watan Yuni daga gobe Litinin 10 ga watan Yuni saboda yin bukukuwan sallah cikin walwala.
An bayyana yadda wasu mutane suka mutu a jihar Legas yayin da masallaci ya rushe a kansu suna tsaka da sallah a wani yankin jihar da ke Kudancin Najeriya.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba ma’aikatan jihar kyautar N15,000 da bashin N30,000 domin bikin sallah cikin walwala ba tare da matsala ba.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa an ga jinjirin wata kuma ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni za zama 1 ga watan Dhu Hijjah.
Bikin Sallah
Samu kari