Bikin Sallah
Babban lomamin jami'ar LASU, Farfesa Amidu Sanni ya bukaci musulmi su guji cin bashin kudi domin cika ibadar layya, yana mai cewa an ɗauke wa wanda ba shi da hali.
A labarin nan, za a ji cewa Fadar Nasarawa da Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero ke jagoranta ta fitar da abubuwan da za Su wakana da Sallah babba a madadin hawa.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dage kan yin addu'o'i game da matsalolin tsaro da sauransu a Najeriya.
Dan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya koma gida jihar Kano domin yin idin babbar sallah, a jiya Laraba, 4 ga watan Yuni.
Malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Farfesa Rashid Abdulganiy ya fadi hukuncin yin sallar Juma'a da azahar a ranar Idi. Malamin ya ce za a yi sallar azahar.
Gwamnatin jihar Kano ta ja hankalin mutane su yi taka tsan-tsan wajen layya, su tabbata sun yanka dabbobi musu lafiya don gujewa ɗaukar cututtuka.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya sanar da hana hawan sallah da duk wasu shagulgula domin zaman makoki da alhinin mutanen da suka mutu a ambaliyar Mokwa.
Rundunar ƴan sanda ta jaddada cewa haramcin hawan sallah da ta ƙaƙaba tun karamar sallah yana nan daram saboda barazanar tsaron da ake hange tana nan.
Yayin da aka sha fama da fari a kasar Morocco, Sarki Muhammad VI ya bukaci marasa karfi a kasar da su dakatar da yin layyan bana saboda tsadar rayuwa.
Bikin Sallah
Samu kari