Sabon Farashin Man Fetur
Matatar man Dangote da sauran masu tace mai sun koka kan matakin da dillalan man suka dauka na cigaba da shigo da mai daga ketare wanda ba shi da kyau.
Tsohon shugaban NESG, Kyari Bukar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen tuge tallafin man fetue shiyasa aka shiga ƙangin wahala.
Daga dawowar shugaban kasa ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, kudin fetur, zaben Edo da ASUU. Daga cikin bukatun da ASUU ke da su akwai biyan albashin malamanta.
Kungiyar kwadago ta ce Bola Tinubu ya so biya musu kudin jirgi domin zuwa kasahe su ji kudin man fetur amma suka ki kar ace sun karbi cin hanci da rashawa.
Kungiyar kwadago ta ce N70,000 da za a biya ma'aikata ba za ta tsinana komai ba kasancewar an kara kudin fetur. Shugaban yan kwadago ya ce za su zauna da Tinubu
Kungiyar yan fansho ta yi watsi da mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta yi. Sun bukaci yan kwadago su tilasta gwamnati biyan N250,000.
A wannan labarin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara sa ido kan wasu 'yan kasuwa a kasar nan domin tabbatar da cewa ba a cutar masu sayen kayayyaki.
Matatar Dangote ta musa kamfanin NNPCL kan adadin man fetur da ta tace. NNPCL ya ce ya loda lita miliyan 16.8 amma matatar Dangote ta ce lita miliyan 111 ne.
Kungiyar 'yan majalisar wakilai marasa rinjaye ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage farashin fetur. Kungiyar ta ce tsadar ta yi yawa duba da halin da ake ciki.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari