Hotunan Rahama Sadau tare da su Akon
Korarriyar 'yar fim din Hausa na kamfanin Kannywood, Rahma Sadau ta amsa gayyatar da shahararen mawakin nan na kasar Amurka, Akon ya yi mata zuwa kasar Amurka.
Rahama Sadau ta kasance fitacciyar jarumar Kannywood wacce aka kora daga Kannywood saboda ta fito a kasetin wakar da ClassiQ yayi inda ta rungume shi. Labarin ya samu cece-kuce ya kuma ja hankalin mutane da dama.
Kamar yadda muka kawo maku a baya cewa jarumar ta rubuta a ranar 15 ga watan Oktoba a shafinta na Tweeter cewa ta samu takardan gayyata zuwa Hollywood na kasar Amurka.
Inda zata kasance tare de babban mawakin kasar Amurka, Akon wanda baya bukatar a sanar ko wanene shi. Ya kasance mawaki mai nasarori yana kuma amfani da fasaharsa a wasan Hollywood kamar irinsu Black November.
Jarumar dai ta samu rakiyar Jeta Amata wanda ya karbi lambar yabo na shirya fina-finan Najeria wanda ke zaune a kasar Amurka.
KU KARANTA KUMA: Anyiwa yar Buhari ba’a kamar yadda ta zama mata ta 4
Ga hotunan jarumar tare da su Akon:
KU KARANTA KUMA: Wani nakasashen mutumi ya auri kyayyawan mata
Asali: Legit.ng