Haduran mota a Najeriya
Hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar hatsarin mota Gulf ranar Jumu'a a titin Kaduna zuwa Abuja, mutum 6 suka rasu.
Wata ɗaliba mai shekara 10 a duniya ta rasa ranta bayan motar wani malamin da ke koyarwa a makarantarsu ta tunkuɗe ta lokacin da take tsaka da yin wasa.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da mutane da dama akan titin hanyar Legas zuwa Ibadan. Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu da dama suka raunata.
Rai bakon duniya, Allah ya yi wa mataimakiyar babban sakataren kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, Esther Ezeama, rasuwa sakamakon hatsarim mota.
Shugaban majalisar dokokin jihar Osun, Adewale Egbedun, ya shallake rijiya da baya yayin da tawagar motocinsa suka gamu hatsari yayin barin Osogbo ranar Lahadi.
Gobara ya yi kaca-kaca da wani sashe a kamfanin robobi na Mega Plastics da ke jihar Legas. An bayyana yadda aka ga kayayyaki sun konje kurmus a kamfanin.
Jimami yayin da mawaki Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya yi hatsarin mota a kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jiragen sama a yau Juma'a 22 ga watan Satumba.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Imo ya salwantar da rayukan mutum uku. Wata motar bas ce dai mai ɗauke da fasinjoji hatsarin ya ritsa da ita.
Wani jami'in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ya rasa ransa bayan wani direban babbar mota ya murƙushe shi yana tsaka da aikinsa a jihar Legas.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari