Sarkin Kano
Babbar kotun jihar Kano ta umarci sarakuna 5 da aka tsige a Kano su mayar da kayan sarautar da ke hannunsu ga Gwamnatin jihar ko Sarki na 16 Muhammadu Sanusi.
Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta kawo karshen rikicin masarautar Kano, ta yanke hukunci a yau Litinin na haramtawa Sarki Ado Bayero bayyana kansa da sarki.
Gamayyar kungiyoyin matasan Kano (KYC) ta yi ikirarin cewa gobarar da ta tashi a fadar Sarkin Kano Sanusi II ya nuna cewa ubangiji bai ji dadin dawo da shi ba.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki matakin rushe masarautu saboda cika alkawuran kamfe da ya dauka.
Ana fargabar gobara ta jawo asara mai tarin yawa a fadar Sarkin Kano bayan iftila'in da ya faru a daren jiya Juma'a 12 ga watan Yuli 2024 a fadar da ke Kofar Kudu.
Wasu fusatattun mazauna masarautar Rano a jihar Kano sun kori wakilin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tura zuwa masarautar da aka rushe.
Wanda ya assasa kuma shugaban cocin ruhaniya na INRI, Primate Elijah Ayodele, ya ce ubangiji ne ya lamunce Muhammadu Sanusi II ya zama sarkin Kano.
Mazauna garin Rano dake jihar Kano sun shiga tashin hankali bayan da aka girke 'yan daba da makamai a masarautar garin. Sun ce basu san wanda ya girke su ko manufa.
Kungiyar Progressives Front of Nigeria (ProFN) ta gargadi jam'iyyar NNPP da Rabiu Musa Ƙwankwaso kan bata sunan Shugaba Bola Tinubu saboda rikicin masarautar Kano.
Sarkin Kano
Samu kari