Sarkin Kano
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanar da cewa za ta ci gaba da zaman shari'ar kan rigimar sarautar Kano da misalin karfe 2:00 na rana yau Alhamis.
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da mutuwar wani mutum guda daya tare da jikkata jami'anta biyu yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar Kano.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tsara yanke hukunci kan ingancin canja dokar masarautar Kano wanda Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi domin daso da Sanusi II.
Rundunar ƴan sanda ta yi kira ga mazauna jihar Kano su zauna lafiya yayin da ake jiran hukuncin Babban Kotun Tarayya kan rigimar sarauta yau Alhamis.
Majasar dokokin jihar Kano ta ɗaukaka ƙara kan dokar masarauta wadda ta saukw sarakuna biyar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa a lokacin mulkinsa.
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce wasu makiya jihar Kano suna ba Gwamnatin Tarayya shawara tare da nuna goyon baya ga Aminu Ado Bayero.
Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso jagoran jam'iyyar NNPP kuma madugun Kwankwasiyya, ya yi zargin cewa makiyan jihar Kano na kokarin kawo hargitsi a jihar.
Lauyan kare hakkin dan Adam kuma babban lauyan Najeriya, Femi Falana, ya ce babbar kotun tarayya da kotun masana’antu ta kasa ba su da hurumin kan al’amuran sarauta.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da sakon barka da Sallah ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Sakon na zuwa ne yayin da ake rikicin sarauta a jihar.
Sarkin Kano
Samu kari