Albashin ma'aikatan najeriya
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamna Umo Eno ya amince zai biya sabon albashin N80,000.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince zai biya ma'aikatan fiye da N70,000.
Abba Kabir Yusuf zai sanar da mafi karancin albashi da zai rika biya a jihar Kano. Abba ya karbi rahoton kwamitin karin albashin ma'aikatan jihar Kano.
Gwamnatin jihar Abia ta shirya fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000. Gwamnatin za ta fara biyan albashin a watan Oktoba.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa yan kwadago sababbin alkawura kan karin kudin fetur. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar an yi karin albashi a dukkan jihohi.
Gwamnatin jihar Lagos ta amince da biyan mafi ƙarancin albashin N85,000 inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce zai kara mafi ƙarancin albashin zuwa N100,000.
An tattara jerin gwamnonin Najeriya da ke biyan mafi karancin albashi fiye da na gwamnatin tarayya. An yi mamaki yadda gwamnatin Gombe za ta biya fiye da N70,000.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya amince da biyan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamnan ya amince zai biya N73,000 a matsayin albashi.
Ma'aikatan jihar Jigawa sun shiga rudani bayan an yi musu ta leko ta koma kan mafi karancin albashi. Gwamna Umar Namadi ya musanta amincewa da N70,000.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari