Albashin ma'aikatan najeriya
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ƙaryata rade-radin da ake yaɗawa cewa ya yi karin mafi karancin albashi ga ma'aikata har N70,000 a jihar.
An yada wani rubutu a shafukan sada zumunta cewa gwamnatin tarayya za ta fara biyan albashin ma'aikatan jihohi da kananan hukumomi. An gano gaskiya.
Kusan dai babu mai goyon bayan gwamnatin tarayya a kan karin kudin wuta. Kungiyar ma’aikatan lantarki ta roki a soke karin kudin lantarki ko su tafi yajin-aiki.
Gwamnatin Jigawa ta amince da N1.1bn domin siyan kayan abinci da suka hada da shinkafa da taliya domin sayarwa ma’aikatan gwamnati kan farashi mai rahusa.
Malamin makaranta ya bada labarin yadda Gwamnati ta wahalar da shi bayan bautar shekara 35 a Kogi. Imam Odankaru ya yi ritaya, yana kukan cewa bai da komai.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya amince da fitar da kudi domin ba ma'aikatan jihar su kwaranniyar watan azumin Ramadan da bikin Sallah.
Bola Tinubu zai sanar da karin albashin Ma’aikata a Ranar 1 ga Mayu. Abin da ake tunani shi ne Tinubu zai sanar da mafi karancin albashin da za a koma amfani da shi
Dangane da karin albashi, kungiyar 'yan fansho ta NUP ta koka kan cewa har yanzu akwai tsofaffin ma'aikata da ake biya N1,500 a wata matsayin kudin fansho.
Bayan janye tallafin man fetur wanda ya haifar da tsadar rayuwa a Najeriya, akwai gwamnonin jihohi 12 da suka yi karin albashi. Legas da Ondo na biyan N35,000.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari