Hukumar Sojin Najeriya
Sace tsohon Manjo din soja, Joe Ajayi mai shekaru 76 a Kogi ya jefa al'ummar garin Odo-Ape cikin fargaba, tare da ƙara tabbatar da matsalar tsaro a yankin.
'Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari a Ijaha Ikobi, jihar Benue, inda suka kashe sojoji biyu da fararen hula biyu. An fitar da gawarwarkin daga yankin.
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce gwamnatinsa na daukar sababbin matakai domin yakar rashin tsaro a fadin jihar baki daya duba da ƙaruwar matsalar.
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya bayyana cewa akwai ƴan siyasa, sojoji da fararen hula da ke haɗa kai da Boko Haram wajen tayar da zaune tsaye.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce sakacin shugabannin da suka biyo bayan Obasanjo ya haifar da matsalar tsaro a ƙasar nan.
A wannan labarin, za ku ji Shugaba Tinubu ya kaddamar da sababbin helikwafta don magance matsalar tsaro a Najeriya, yayin da ake sa ran karo wasu.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da manyan hafsoshin sojin ƙasar nan da sauran shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati da ke Abuja.
Babban hafsan tsaron kasa, Christopher Musa ya bayyana cewa Najeriya ta shirya kakkabe duk wasu ƴan ta'adda daga doron duniya, ya ce an sayo makamai.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka tun da ya karɓi mulki sun taka rawa wajen inganta tsaro fiye da yadɗa ya tarar a jihar.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari