Labaran tattalin arzikin Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa za a ba talakawa miliyan 10 tallafin a 2026. Za a ba mutum 1,000 a dukkan mazabu 8,809 tallafin a Najeriya.
Sabuwar hukumar tattara haraji ta Najeriya watau NRS ta fara aiki bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu, an fitar da tambarin hukumar.
Ƙungiyar ɗalibai ta NANS ta ayyana 14 ga Janairu, 2026 a matsayin ranar zanga-zangar ƙasa kan sabuwar dokar haraji, tana mai kiran ɗalibai su yi tattaki zuwa Villa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbaci kan lokacin fara aiwatar da sabuwar dokar haraji. Ya ce ba gudu ba ja da baya kan lokacin da aka tsara.
Gwamnonin jihohin Lagos, Abia, Ogun, Enugu, Osun, Delta, Sokoto, Edo, Bayelsa da Gombena shirin ciwo bashin Naira tiriliyan 4.287 a 2026 kan kasafin kudi.
Daga 1 ga Janairun shekarar 2026, bankuna za su fara cire ₦50 harajin hatimi (stamp duty) kan duk wata tura kuɗi ta lantarki daga ₦10,000 zuwa sama.
Cikin abubuwan da za su faru a 2026, Aliko Dangote zai fara raba mai kyauta, dokar haraji, cire kudi za su fara aiki, za a yi zabe a Ekiti da Osun, APC za ta yi taro
SERAP ta shigar da karar gwamnoni 35 da Nyesom Wike gaban kotu kan zargin rashin bayyana yadda aka kashe N14tn na rarar kudaden tallafin man fetur.
Bincike ya nuna cewa babu wata doka da aka tanada a sababbin dokokin haraji da ke nuna cewa an ware musulmai, ba za su rika biyan haraji ba a Najeriya daga 2026.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari