Hukumar Kwastam
Hukumar kwastam ta yi alwashin kawo karshen masu boye kayan abinci a Najeriya domin kawo saukin kayan masarufi. Shugaban hukumar, Wale Adeniyi ne ya fadi haka.
Hukumar kwastam ta ce ta gano jami'anta da suke taimakawa dilolin kwaya wajen shigo da haramtattun kayayyaki Najeriya. Shugaban hukumar ne ya fadi haka.
Hukumar kwastam ta kama masu safarar man fetur daga Najeriya zuwa kasashen ketare inda ta kama lita 150,950 da ya kai N105.9m a Adamawa, Sokoto da Cross Rivers
Yayin da ake fama da tsadar kayan abinci, gwamnatin tarayya na shirin dakatar da harajin shigo da wasu muhimman kaya irinsu kayan abinci cikin kasar nan.
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji ya bawa gwamnatin tarayya shawara kan sabon harajin kayan dake shigowa kasar.
Jami'an hukumar hana fasakwauri ta bayyana dakile yunkurin shigo da buhunhunan shinkafa 'yar waje akalla 6,467 ta iyakar Seme wanda ya kai tirela 10.
Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce abokan huldarsa a kasashen ketare sun hana su kuɗin wutar da suka sha wanda ya kai $51m a shekarar 2023.
Yan bindiga sun kai hari anguwar Shagari da ke Dei- Dei a birnin tarayya Abuja tare da yin garkuwa da jami'in kwastam da matarsa da 'ya'yansa guda uku.
Hukumar hana fasa kwauri ta ce ta damke lita 12,435 na man fetur wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 10.8 a hanyar Cameroon. An kuma kama jarka 61 a hanyar Benin.
Hukumar Kwastam
Samu kari