Jihar Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana rashin jin dadin yadda masu muhawara a kan kudirin harajin gwamnatin tarayya ba su san yadda abin ya ke ba.
A wani lamari na bazata, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sallami Sakataren Gwamnatinsa tare da rusa majalisar zartaswa da sauran hadimai.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya dakatar da shugaban hukumar kula da harkokin malamai watau TSC kan vadakalar ɗaukar sababin malaman makaranta 1,000.
An samu tashin wata mummunar gobara a jihar Nasarawa. Gobarar ta tashi ne a wata fitacciyar kasuwa inda ta lalata shaguna da kayayyaki na miliyoyin Naira.
Sanata Ahmed Wadada ya karyata zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na neman kawo cikas ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya ta hanyar kudirin gyaran haraji.
Matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta raba tallafin miliyoyin kudi ga tsofaffi a Arewa, Gombe da Nasarawa. Tsofaffi 500 ne suka samu tallafin N50m.
Gwamnonin Najeriya sun shawarci hukumomi a kan yawan hadurra. Wannan na zuwa bayan mutuwar mutane 20 a Binuwai. Gwamnonin sun kara da mika ta'aziyya ga gwamnati.
Bankuna a jihar Nasarawa sun rage cire kudi, wanda ya jawo masu POS ke caji mai tsada. Jama'a sun fara korafi yayin da suke fuskantar wahala saboda karancin kudi.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jira ya kare domin ma'aikata za su fara ganin sabon mafi ƙarancin albashi na N70,500 a karshen watan Disamba.
Jihar Nasarawa
Samu kari