Nadin Sarauta
Bayan zargin batanci da ake yi masa, wata kotu a Ede da ke jihar Osun, ta bayar da umarnin tsare wani babban basarake da aka dakatar, Jimoh Abdulkabir.
A wannan labarin, za ku ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gudanar da Hawan Fanisau a yanayin da ya dauki hankalin jama'a a Kano.
Yayin da ake bukukuwan sallah, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar mawaki Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) daga Ɗan Amanan Bichi zuwa Ɗan Amanan Kano
Rikicin sarauta ya sake barkewa a kauyen Muye da ke ƙaramar hukumar Lapai, ta jihar Niger bayan tsohon dagacin kauyen ya koma fada da karfi domin kwace kujerarsa.
Rahotanni da muka samu sun ce rigima ta sake kunno kai a masarautar Zazzau bayan majalisar dokokin Kaduna ta karɓi ƙorafin cire Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon Sarkin Gwandu, Al-Mustapha Jokolo ya ce ya rungumi kaddara bayan kotun koli ta tabbatar da raba shi da sarautar Gwandu baki daya.
Bayan shafe shekaru 20 ana tababa kan sarautar Gwandu da ke jihar Kebbi, Kotun Koli ta kawo ƙarshen rigimar inda ta soke dawo da Al-Mustapha Jokolo kan karaga.
Kotun kolin Najeriya ta matso da ranar yanke hukunci kan dambarwar masarautar Gwandu da ke jihar Kebbi saboda hutun sallah, za a yanke hukunci ranar Laraba.
Mun samu rahoton cewa jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar wani mai gadin fada bayan wani gangamin dawakai ba bisa ka’ida ba a Gumel, jihar Jigawa.
Nadin Sarauta
Samu kari