Nadin Sarauta
Lamari ya fara daukan zafi a jihar Osun bayan kama Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede. Mutanen yankin sun bukaci a sauya Sarkin da gaggawa bayan daure shi.
Rahotanni daga masarautar Ipetumodu ta nuna cewa an fara duba yiwuwar tube rawanin Sarki bayan kotun Amurka ta daure shi na tsawon watanni 56 a gidan yari.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya amince da da naɗin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru, don ya gaji marigayi Muhammadu Sani Sami Gomo II.
Sarkin Irokun, Oba Buari Ola Balogun da ke jihar Ogun ya bukaci gwamnatin Ondo ta daina yunƙurin da ya kira ba bisa ka’ida ba na naɗa sabon Sarki a yankin jihar.
Sarkin Iwo da ke jihar Osun a Kudu maso Yamma a Najeriya, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi Allah wadai da masu yada jita-jitar cewa yana shan tabar wiwi.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na iya tsige mai martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede bayan kotun Amurka ta daure shi na tsawon shekaru.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya amince da kirkiro karin sarakuna uku domin karfafa ayyukan masarautun gargajiya a jihar Kogi, ya dawo da sarkin Omala.
An fara fafutukar neman kujerar sarkin Ijebu da ke jihar Ogun bayan rasuwar Mai Martaba Oba Sikiru, kawo yanzu mutane 17 sun nuna sha'awar hawa karagar mulki.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar IIIya taya sabon sarkin Ibadan murna tare da yi masa fatan alheri wajen sauke mauyin da ya hau kansa.
Nadin Sarauta
Samu kari