Nadin Sarauta
A ranar talata, 28 ga watan Mayu, babbar kotun tarayya a Kano ta ba da umarnin korar Sarkin Kano Sanusi II daga fa, yayin da babbar kotun jihar ta hana yin hakan.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya takunkumi mai tsauri kan duk wani taron jama'a da aka shirya da nufin gudanar da zanga-zanga a fadin jihar.
Wasu lauyoyi, wadanda suka bayyana kan su a matsayin 'kungiyar lauyoyin Arewa' sun ba gwamnan Kano Abba Yusuf wa'adin awa 48 ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi II.
Ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba shi ne karon farko da Mai shari'a A.M Liman ya shiga cikin cakwakiya ba.
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya fito daga fadar sarki da ke Nasarrawa yau Litinin, 27 ga watan Mayu, 2024, bidiyo ya bazu a soshiyal midiya.
Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta labarin da ke cewa ‘yan majalisar sun karbi cin hanci domin rushe masarautun jihar biyar da nada sabon sarki.
Magoya bayan sarakuna biyar da gwamnatin jihar Kano ta tube rawunansu sun gudanar da Sallar Al-Qunut tare da yin addu'ar Allah ya mayar da sarakunansu.
Kamar yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada tare da hakimai a yau Lahadi an ce shi ma Aminu Bayero, tsohon Sarkin Kano, ya yi zaman fada a Nassarawa.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya samu goyon bayan hakimai 40 cikin 65 na jihar. Hakan na nufin cewa mafi rinjayen hakiman Kano sun yi mubayi'a ga sabon sarki.
Nadin Sarauta
Samu kari