Musulmai
Kungiyar addinin Musulunci MURIC mai gwagwarmayar kare hakƙin al'ummar Musulmin Najeriya ta nanata cewa har yanzun kujerar Sarkin Musulmi na tsaka mai wuya.
Kudurin sabunta dokar Masarautar Sokoto ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren majalisar Sokoto. Ana fargabar kudurinzai rage ikon Sarkin Musulmi
Kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano ta ziyarci fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II domin nuna goyon bayansu gare shi bayan dawowa kujerar sarauta.
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Gwamna Ahmed Aliyu ta musanta zargin cewa tana wasu shirye-shirye ta bayan fage domin sauke Mai alfarma Sarkin Musulmi.
Rundunar sojojin Nigeria ta ƙaryata rade-radin cewa tana daukar Musulmai masu tsattsauran ra'ayi aikin soja kamar yadda ake yadawa cewa suna kare addinin Musulunci.
Kasar Saudiyya ta amince da nadin Sheikh Abdulwahab Al-Shaibi a matsayin sabon mai rike makullin ɗakin Ka'aba. Shi ne na 110 a tarihin masu rike makullin
Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi zargin cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya haramta tare hanyoyi da wasu ke yi yayin ibadar Musulmai ko Kiristoci a fadin jihar baki daya domin samun daidaito.
Jirgin farko da ya kwaso alhazan Najeriya daga Saudiya ya Iso gida. Kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana sun dawo gida.
Musulmai
Samu kari