Musulmai
Gwamnati ta rufe masallacin Hausawa na Agege da ke Legas yayin da bangarori uku ke takaddama kan wanda zai gaji marigayi babban limamin masallacin.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan 'Quranic Festival', shugaban kungiyar Izalah bangaren Kaduna ya yi martani ga Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalamansa.
'Yan sanda sun kama barawon da ake zargi da sace kayan masallaci da suka kai N520,000. Barawon ya sace fankoki da tagoggin masallacin ya sayar da su.
Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya. Yayin da Musulmai suka nuna goyon baya, Yarbawa sun ce ba su yarda ba.
Kungiyar Izala ta yi martani ga Sheikh Muhammad Bin Usman Kano kan masallacin Sahaba. Wanda ya gina masallacin ya ce sharrin shaidan ne ya kawo sabanin.
Gwamnatin Jigawa ta ware Naira biliyan 4.8 don ciyar da mabukata 189,000 a Ramadan. Haka kuma, za a gyara asibitoci 114, wanda zai ci Naira biliyan 9.7.
Yayin da watan Azumi ke kara gabatowa, Majalisar Sarkin Musulmi ta umarci al'ummar Musulmi da su fara duba watan Sha’aban 1446 AH a gobe Laraba, 29 ga Janairun 2025.
Wasu 'yan Izala a kafafen sada zumunta sun yi rubdugu da shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo kan bikin Qur'anic Festival da aka shirya a Abuja.
Hukumar kula da alhazai ta jihar Kwara ta ce ranar ƙarshe ta biyan kuɗin Hajjin 2025 ita ce Janairu 31, 2025. An nemi alhazai su gabatar da fasfo kafin Fabrairu 25.
Musulmai
Samu kari