Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun yan bindiga dauke da makamai sun kai wani sabon hari a jihar Benue. Yan bindigan a yayin farmakin na su sun salwantar da rayuka tare da tafka barna.
Wasu rubuce-rubuce da aka yi a shafin Facebook sun yi ikirarin cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya na raba tallafin bashin N500,000 ga yan Najeriya.
Jam'iyyun PDP da LP sun fito sun yi suka kan tafiyar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi zuwa kasar Faransa. Sun bayyana cewa akwai lauje cikin nadi.
Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkar manufofi da tabbatar da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman ta ce akwai Ministocin tarayyan da Shugaba Tinubu zai rabu da su.
Ola Olukoyede,shugaban hukumar EFCC, na fuskantar barazanar dauri a magarkama. An tattaro cewa Olukoyede da hukumar EFCC sun ki bin wani umurnin kotu.
Bayanai sun bayyana kan yadda kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta tsige Ayo Adebanjo a matsayin mukaddashin shugabanta a gidan jagoranta, Pa Reuben Fasaranti.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar LP a zaben gwamnan 2023 a jihar Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour, ya tabbatar da biyan kudin da tsohon ma’aikacin matarsa ke bin ta.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya nada tsohon mataimakin magatakardar majalisar dokokin tarayya, Olayide Owolabi Adelami a matsayin gwamnan jihar Ondo.
Wani sabon rikici ya barke a jihar Plateau. Sabon rikicin wanda ya barke a karamar hukumar Mangu ta jihar ana fargabar ya jawo asarar rayuka masu yawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari