Mai Mala Buni
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya nuna damuwarsa kan rikicin Boko Haram. Gwamnan ya ce talauci da jahilci na taka rawa wajen ruruwar da rikicin ke yi.
Bayan yada jita-jitar komawar wasu gwamnonin APC zuwa tafiyar Atiku Abubakar, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce ba zai taba barin jam'iyyarsa ba.
Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta bayyana cewa ta shirya shigar da tubabbun 'yan ta'addan Boko Haram cikin al'umma.
Gwamnatin jihar Yobe ta nemi jama'a su kwantar da hankalinsu bayan ta karyata labarin cewa ƴan Boko Haram sun ba wasu wa'adi su fice daga cikin garuruwansu.
Wani babban jigo a jam'iyyar APC a jihar Yobe, Sa'idu Hassan Jakusko, ya sanar da ficewarsa daga APC. Ya nuna cewa ba a saka musu ba duk da wahalar da suka yi.
Gwamnan jihar Yobe ya raba tallafin kudi ga wasu talakawa masu aikin saran itace, matafiya da masu aikin titi. Gwamnan ya raba kudin ne yayin ziyarar ba zata.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya koka kan yadda jami'an tsaro ba su kawo rahotanni kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu. Ya ce hukumomi ba su yin aikinsu.
Gwamna Mai Mala Buni ya dauki ma'aikatan lafiya kimanin 424 a jihar Yobe domin inganta rayuwar al'ummar jihar. Ya ce zai cigaba da kula da harkar lafiyar al'umma.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kafa sabuwar ma'aikatar kula da kiwon dabbobi. Gwamnan ya umarci a samar da dukkanin abubuwan da take bukata.
Mai Mala Buni
Samu kari