Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga yayin wani artabun da suka yi a jihar Kano. Sojojin sun kuma kwata kayayyaki.
Hukumar leken asiri ta gano N11bn a asusun wani kanal da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki, lamarin ya kara tsananta bincike kan lamarin.
Dan takarar shugaban kasa a SDP a zaben 2023. Adewole Adebayo ya ce babu wani alheri da za a samu a mulkin soja a Najeriya. Ya ce dimokuradiyya ta fi.
Wasu rahotanni sun ce hukumar EFCC da NFIU sun fara bincike kan yadda aka so amfani da wasu kudi a shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cocin HEKAN a Kaduna ya tabbatar da cewa an kashe Fasto Yahaya Kambasiya tare da sace mutane sama da 20 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar tsaron kasar nan ta yi sauye-sauye da dama, inda aka canjawa manyan sojoji akalla 67 wuraren aiki bayan nada hafsoshin tsaro.
Fadar shugaban kasa ta gargadi 'yan Najeriya kan yada labarun juyin mulki marasa tushe. Nayo Onanuga ya ce yada labarin zai jawo bata sunan Najeriya a duniya.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci hafsoshin tsaro su zage damtse su magance barazanar tsaron da ke kara taaowa a wasu sassan kasar nan.
Rahotanni daga rundunar sojin Najeriya na nuna cewa sojojin da aka tsare kan zargin shirya juyin mulki a Najeriya sun karu zuwa 42, ana ci gaba da bincike a kansu.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari