Zaben jihohi
Tsohon Minista Hadi Sirika ya ayyana neman kujerar Sanata a Katsina ta Arewa yau 24 ga Afrilu, 2026, sakamakon kiraye-kirayen al'ummar shiyyar Daura.
Jam'iyyar APC za ta fara sayar da fom din takara daga 25 ga Afrilu, 2026, sannan za ta gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa a ranar 23 ga Mayu.
Hukumar INEC ta fara shirin zaɓen 2027 a yau 23 ga Afrilu, 2026, inda ta ba jam'iyyun siyasa wa'adin kwanaki 38 domin gudanar da zaɓukan fitar da gwani.
Tsohon shugaban APC a Kwara, Bashir Bolarinwa, ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna, yana cewa yana da kwarewa da hangen nesa don magance matsalolin jiha.
Hukumar INEC ta matsar da ranar kammala yaƙin neman zaɓen gwamnan Osun zuwa 13 ga Agusta, 2026, bayan sauya ranar zaɓen zuwa 15 ga watan. An gargadi jam'iyyu.
Gwamna Abdullahi Sule ya ayyana Sanata Ahmed Wadada a matsayin wanda zai gaje shi a zaɓen 2027 domin ci gaba da mulkar jihar Nasarawa karkashin jam'iyyar APC.
A labarin nan, za a ji lamari na neman rikcabewa gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf game da wanda zai nada a matsayin mataimakinsa bayan Gwarzo ya yi murabus.
Kotu ta hana Gwamna Aiyedatiwa tsaya wa takara a 2028 a jihar Ondo. An ce barin sa takara zai saba wa dokar wa'adin shekaru 8 na mulki a Najeriya.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da jerin jam'iyyun da za a fafata da su a zaben gwamnan Osun dake tafe.
Zaben jihohi
Samu kari