Labaran garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sandan Najeriya da ke jihar Edo ta yi nasarar kashe wani da ake zargi da garkuwa da mutane. Za a kafa kotu domin hukunta 'yan ta'adda.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen jihar na dauko hayar miyagu domin aikata laifuffukan garkuwa da mutane.
Babbar kotun jihar Kogi ta sami wani jagoran dabar yan bindiga, Jibrin Halilu da laifin garkuwa da makwabcinsa tare da kashe shi, ta umarci a rataye shi.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya da hadin gwiwar jami'an tsafo sun yi nasarar ceto mutane hudu daga hannun masu garkuwa da mutane, an kai su asibiti.
Rahotanni sun nun cewa wani fitaccen dan kasuwa kuma manomi a karamr hukumar Dandume ta jihar Katsina ya rasa ransa bayan yan bindiga sun sace shi.
An sanar da cewa Mai Martaba Alhaji Olatunji da aka sace a jihar Kwara ya rasu. An sanar da cewa iyalan sarkin sun biya 'yan bindigar da suka sace shi kudin fansa.
Waua majiyoyi biyu sun yi bayani mai cin karo da juna kan yadda aka dauko gawar Manjo Janar Rabe Abubakar mao ritaya bayan ya rasu a hannun masu garkuwa.
Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu ne a hannun 'yan bindiga bayan fiye d kwanaki 10 da sace shi a Katsina, tuni aka dauko gawarsa aka birne shi a Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa duk da rasuwar tsohon Manjo Janar na sojoji, Rabe Abubakar, yan bindiga sun ci gaba da tsare matarsa, Hajiya Amina Abubakar.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari