Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Bayan yan uwan dan TikTok mai yada badala sun hukunta shi, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jinjina musu inda ya bukaci a yi koyi da su cikin al'umma.
Wani dan Arewa a shafin sada zumunta ya nuna goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hakan ya sanya mutane da dama sun yi masa rubdugu.
Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce kwata-kwata bai iya munafurci a siyasa ba kuma ba zai zama kamar yan wasan kwaikwayo a gwamnati ba.
An fara waiwayen yadda ma'aikatar sadarwa karkashin jagorancin Farfesa Isa Ali Pantami a gwamnatin Muhammadu Buhari ta dakile yunkurin karin kudin waya.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai 'yan kasar nan za su kashe sama da Naira biliyan 6 a 2025 bayan karin kudin kiran waya da gwamnati ta amince da shi.
Kungiyar SERAP ta shigar gwamnatin Bola Tinubu da gwamnoni 36 a kotu kan amfani da dokar laifuffukan yanar gizo (Cybercrimes) don tauye 'yancin fadin albarkacin baki
Gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sadarwa su yi ƙarin kudin kiran waya, sako da sayen data amma ba zai kai kaso 100% ba in ji ministan sadarwa, Bosun Tijani.
Ministan sadarwa na Najeriya, Bosun Tijani ya shiga taro da wakilan kamfanonin sadarwa da ke aiki a kasar nan kan bukatarsu na kara kudin kira da data.
Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun yi koken cewa hauhawar farashi a kasar ya shafe su, saboda haka ne suke bukatar a sahale masu karin farashin waya.
Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Samu kari