Kasashen Duniya
Hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) ta samu nasarar damke wani mai safarar mutane, a kokarin fitar da su wajen kasar nan, inda yanzu haka ake zurfafa bincike.
Matashiyar yar kasuwa kuma jaruma a shirin BBNaija, Kate Ka3na Jones ta wallafa a shafinta na Instagram yadda ta samu makudan miliyoyin daloli a dare daya.
Yayin da ake jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, Amurka ta nuna damuwa kan yadda marigayin ya bar duniya da alhakin mutane da dama.
A jiya Lahadi, shugaban ƙasa, Ebrahim Raisi da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar Iran suka gamu da hatsarin jirgin sama wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
A yayin da ake zaman makokin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, an ruwaito cewa girgizar kasa mai karfin 3.7m ta afku a yammacin kasar Iran a yau Litinin.
Shugaban juyin juya hali na kasar Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya sanar da cewa za a yi kwanaki biyar ana zaman makokin shugaban kasar, Ebrahim Raisi da ya rasu.
Bayan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, mahukunta sun nada mataimakinsa, Mohammad Mokhber, a matsayin shugaban riko har zuwa a gudanar da zabe.
A yayin da aka tabbatar da mutuwar Ebrahim Raisi, shugaban kasar Iran da mukarrabansa a wani hatsarin jirgin sama, mun tattara abubuwan da ya kamata ku sani.
A yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi, a hannu daya kuma, an kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti saboda cutar huhu.
Kasashen Duniya
Samu kari