Kasashen Duniya
Hukumar hana fasa kwauri ta ce ta damke lita 12,435 na man fetur wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 10.8 a hanyar Cameroon. An kuma kama jarka 61 a hanyar Benin.
A cikin shekara 1, Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci kasashe 14 a tafiye-tafiye 20 da ya yi zuwa kasashen waje. Mun tattara jerin ƙasashen da dalilin tafiye-tafiye.
Kungiyar ALDRAP ta maka mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da sauran sanatoci 39 kan kasancewa mambobin majalisu 2 mabambanta.
'Yan jarida na taka rawa wajen samar da bayanai da rahotanni ga al'umma. Sai dai akwai kasashen da ba su da cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Akalla ma'aikata 200 ne ake fargabar za su rasa aiki a yayin da babban kamfanin kimiya na kasar Amurka, Microsoft, ya fara shirye-shiryen rufe ofishinsa na Najeriya.
Yayin da aka shafe sama da mako ɗaya Tinubu bai dawo Najeriya ba bayan taron Saundiyya, mun gaɗa muku abubuwan da tafiyar da shugaban ƙasar ya yi ta kunsa.
Gwamnatin tarayya ta yi martani kan wani rahoto da ake yadawa na cewa tana tattaunawa da Amurka da Faransa kan kafa sansanonin sojinsu bayan barin yankin Sahel.
Sojojin Nijar sun cafke kasurgumin dan bindigar nan na Najeriya, Kachallah Mai Daji a Illela a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar.
Sakamakon dumbin bashin Naira biliyan 132.2 da kuma yunkurin cimma bukatun gida, Najeriya ta takaita tura wutar lantarki zuwa zuwa Benin, Niger, da Togo.
Kasashen Duniya
Samu kari