Kasar Saudiya
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa domin tafiya kasa mai tsarki gudanar da aikin Hajjin 2024.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da cewa za ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024 zuwa kasa mai tsarki.
Biyo bayan yawaitar mutuwar mahajjata a kasar Saudiyya saboda tsananin zafi, an dauki matakan sanyaya yanayi domin rage mutuwar mutane yayin aikin hajji.
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kebbi ta tabbatar da rasuwar wani Alhaji a birnin Makkah na kasar Saudiyya. Alhajin ya rasu ne bayan 'yar gajeruwar jinya.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wata mata mai suna Hajiya Hawawu daga Kwara ta rasu, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa ta yi ajalin kanta.
Gwamnatin jihar Kano ta samar da asibiti a kasa mai tsarki domin duba Alhazan jihar masu gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024 a Saudiyya.
Gwamnatin jihar Kano ta ƙara ɗaukar matakai da nufin inganta walwala da jin daɗin alhazan jihar na tsawom lokacin da za su ɗauka a ƙasa mai tsarki.
Allah ya yiwa wata Hajiya 'yar Najeriya a birnin Madina yayin gudanar da aikin Hajji. Hajiyar wacce ta fito daga Neja ta rasu ne bayan ta kamu da rashin lafiya.
Jami'an tsaro na musamman sun kama gungun yan damafara masu cutar mutane da sunan sama musu izinin aikin Hajji a Makka. An kama su da abubuwa da dama.
Kasar Saudiya
Samu kari