Karatun Ilimi
Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya ce hadda da karatun Alkur'ani na taimakawa matuka wajen gyara kwakwalwa musamman ga matasa, don haka ya nemi su kara kaimi.
Legit tayi hira da malamin musuluncin da yake koyar da Al-Kur’ani ga kurame. Ustaz Yasir Sulaiman Kofa ya shaida mana yadda suke aiki da kalubalen da ke gabansu.
Gwamnatin tarayya ta ce za ta gina wata makarantar sakandare ta zamani a Abuja, wacce za a kashe naira biliyan 1.7 wajen gina ta, kuma a cikin shekara daya.
Hukumar NDLEA ta ce rahoton da wani jami'in ta ya fitar na cewa kaso 60% cikin 100% na daliban Kano na shan kwayoyi ba gaskiya ba ne, ta ce kuskure aka samu.
Masana harkokin ilimi sun fitar da wasu muhimman dalilai da suka sa ilimi ya gaza a Najeriya musamman a makarantun firamare da yara ba sa iya karatu.
Umar Audu, dan jarida mai bincike ta karkashin kasa ya roki gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bashi tsaro biyo bayan rahotonsa na jami'o'i masu bada digirin bogi.
Shirin 'Fulbright Teaching Execellence and Achievement Program' ya tahowa malamai yan Najeriya da dama na samun aikin koyarwa a Amurka bayan horaswa na sati shida.
Hukumar Kula da Jami'o'i na Najeriya (NUC) ta sanar da cewa ta fara bincike kan wasu jami'o'i 9 a kasar da ake zargin an kafa su ba bisa ka'ida ba.
Shugaban kungiyar NANS reshen jami'o'in Benin, Ugochukwu Favour ya nemi a kama dan jaridan da ya yi rahoton 'digiri dan Kwatano', inda ya ce barazana ne ga gwamnati.
Karatun Ilimi
Samu kari