Jihar Kaduna
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun yi yunkurin bude kwanar Gwargaje da matasa masu zanga zanga suka toshe. Yan sanda sun fesa borkonon tsohuwa ga matasan.
Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan masu zanga-zanga sun haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan toshe titi a Suleja da ke jihar Neja.
Gwamnonin Arewa ta yamma sun shirya taron zaman lafiya a Kaduna domin ba kwamishinonin tsaro horo kan yaki da yan bindiga. Gwamnan Kaduna ya kaddamar da taron.
Gwamnan jihar Kaduna ya bukaci matasa masu shirin zanga zanga su dakata domin tsoron barkewar rikici a lokacin zanga zanga. Nuhu Bamalli ma ya yi kira ga matasan.
Tsohon kwamishina a jihar Kaduna, Alhaji Lawal Yusufu Saulawa ya rasu yana da shekaru 80 a duniya inda aka yi jana'izarsa a yau Lahadi a jihar Kaduna.
'Yan majalisar wakilai daga yankin Arewa maso Yamma sun yi kira ga mutanen yankin da su hakura da fitowa zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a fadin kasar nan.
Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani ya shawarci sarakuna watau shugabannin al'umma su wayar da kan mutane kan illar zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da nasara da ta samu kan yan ta'adda a jihar Kaduna. Sojoji sun fafata da yan bindigar inda suka kashe biyu suka kwato makamai.
Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu ya soki kungiyar da ta yi barazanar masa kiranye inda ya ce ba zai bata lokacin wurin fahimtar da su ayyukan da yake yi ba.
Jihar Kaduna
Samu kari