
Jihar Kogi







Matar shugaban kasa, Oluremi Bola Tinubu ta yi martani kan dambarwar da ke faruwa a majalisa kan zargin da Natasha Akpoti-Uduaghan ke yi wa Godswill Akpabio.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya nuna cewa yana da da alaka mai kyau da mijin Sanata Natasha Akpoti. Ya tuna baya kan aurensu.

Majalisar dattawa ta amince da shawarwarin kwamitin ladabtarwarta, inda ta dakatar da sanatar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha, wadda ta zargi Akpabio da lalata.

Kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawan Najeriya ta ba da shawarin dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya na tsawon watanni 6 kan zargin Sanata Godswill Akpabio.

Masu ruwa da tsaki daga mazaɓar Kogi ta Tsakiya sun barranta kansu da abubuwan da ke faruwa tsakanin Sanata Natasha da shugaban Majalisar dattawa, Akpabio.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi bayani ta bangarensa kan zargin da ake masa na neman Sanata Natasha da lalata, ya ce karya ne.

Ana tsaka da dambarwar Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio, Sanata daga jihar Ekiti ya bankado yadda ta taba zargin tsohon gwamna, Kayode Fayemi.

Bayan korafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wasu Sanatoci sun ki amincewa da kokenta, suna cewa ba a bi ka’idojin majalisa ba, yayin da wasu ke goyon bayanta.

Sanatar Kogi ta Tsakiya ta miƙa takardar korafi a hukumance kan zargin da take wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da neman lalata da ita.
Jihar Kogi
Samu kari