Jihar Kano
Jam'iyyar NNPP ta ce tana fatan Kotun Koli ta kawo karshen wannan dambarwar da ta mamaye hukuncin Kotun Daukaka Kara kan zaben gwamnan jihar Kano.
Yan sanda da jami'an sibil defens sun hana taron addu'o'in da magoya bayan NNPP suka shirya gudanarwa a filin Marhala ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023.
Jam'iyyar APC ta ce tana da majiya mai karfi da ta nuna cewa magoya bayan NNPP na shirin farmakan wasu jiga-jiganta ranar Asabar, ta roki yan sanda su ankara.
Jami'yyar APC ta ce kuskuren da aka samu ya nuna yadda alkalai su ke a matsayin 'yan Adam masu kuskure a hukuncinsu bayan fitar da takardun CTC a ranar Talata.
Bayan barkewar zanga-zanga a jiya Laraba a jihar Kano, jami'yyar APC ta soki takwararta ta NNPP da ingiza mutane don tayar da hankali a jihar bayan hukuncin kotu.
Farfesa Chidi Odinakalu ya ce akwai alaka tsakanin Alkalin da kuma shugaban Alkalin Alkalai na kasa watau Kayode Ariwoola, mun gano akwai alakarsu da manya a APC.
Kwamitin gudanarwa na bankin Musulunci na Ja'iz ya nada Haruna Musa a matsayin sabon shugaban bankin bayan sahalewar Babban Bankin Najeruya, CBN.
Bayanan takardun shari’ar Abba v Gawuna ba kuskure ba ne a ra'ayin wasu. Chidi Odinkalu ya fadawa duniya cewa kotun daukaka kara ba za ta iya yin kwaba ta gyara ba.
Femi Falana, babban lauyan Najeriya, ya ce sabanin tunanin jama’a, kotun daukaka kara reshen Abuja, ba ta soke zaben gwamna Yusuf na jihar Kano ba.
Jihar Kano
Samu kari