Jihar Kano
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tabbatar da dokar da za ta dakile sarakunan gargajiya shiga duk wata yarjejeniya da ta shafi filaye a fadin jihar.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna damuwa kan yadda fadace-fadacen ƴan daba ke kara ƙamari a jihar inda ya ce ya san wadanda ke daukar nauyinsu.
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al'ummar jihar da su guji yin amfani da ruwan sama wanda ba a tsaftace shi sakamakon barkewar cutar kwalara a Najeriya.
Bayan shan suka, fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya wallafa wata hira da Farfesa Mamman Yusufari SAN inda lauyan ya tabbatar da abin da Hikima ya fada.
Yayin da ake ta taƙaddama kan abin ɗa hukuncin babbar kotun tarayya ke nufi, wani mais sharhi kan harkokin yau da kullum, Law Mefor, ya ce Aminu ne Sarki.
A karon farko a tarihin Kano, Abba Kabir Yusuf ya warewa sha'anin ilmi kusan 30%. Hassan Sani Tukur ya ce banagaren ilmi zai tashi da kaso mai tsoka a kasafin kudi.
Hassan Sani Tukur yana cikin wadanda suke taimakwa gwamnan jihar Kano. Legit Hausa ta tattauna da shi bayan Abba Kabir Yusuf ya cika shekara daya a ofis.
Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta zargi APC da neman kawo rudani a rigimar sarauta a jihar Kano domin kwace mulkin jihar karfi da yaji kuma ta kowace hanya.
Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautun Kano, Farfesa Farooq Kperogi ya yi tsokaci kan lamarin inda ya bukaci Abba Kabir ya guji rushe fadar Nassarawa.
Jihar Kano
Samu kari