Hare-haren makiyaya a Najeriya
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a Filato, a wasu hare-haren ramuwar gayya, lamarin da ya tilasta gwamnati ta daukar matakan tsaro na gaggawa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan makiyaya a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka wani makiyayi tare da kashe shanu masu yawa da sace wasu.
Ana fargabar makiyaya sun kashe mutane 9 ciki har da dan sanda a Benue, yayin da matsalar tituna ke hana jami’an tsaro isa cikin gaggawa domin ceto rayuka.
'Yan ta'adda da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kone gidaje 100 a yankin Bandawa Gwenzu na karamar hukumar Karim Lamido a Taraba. Mutum 1 ya mutu.
Gwamna Alia ya tattauna da Tinubu da Akume kan rikicin Binuwai. An nemi sulhu don dakatar da kisan gilla da mayar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Benue na fuskantar hare-haren 'yan bindiga; sama da 100 sun mutu, dubbai sun rasa matsuguni. NEMA na neman agaji yayin da aka kafa sansanin 'yan gudun hijira.
Babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya isa jihar Benuwai, ya tura dakaru na musamman domin daƙile hare-haren da makiyaya ke kai wa.
Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutum 300 ciki har da sojoji sun rasa rayukansu a wani mummunan haru da ƴan bindiga suka kai kauyuka 2 a jihar Benuwai.
An shuga jimami bayan barkewar wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya a jihar Neja. Rikicin ya jawo an samu asarar rai yayin da aka raunata wasu da dama.
Hare-haren makiyaya a Najeriya
Samu kari