Guaranty Trust Bank - Gtbank
Wani ɗan Najeriya ya koka inda ya caccaki bankinsa bayan ya gano cewa makuɗan kuɗaɗen da ya ciro a banki na jabu ne. Kuɗaɗen dai an ba shi su ne a Yuro.
Wani kwastoma ya fusata bayan ya rasa N500,000 a asusun ajiyarsa na banki, keastoman dai ya kinkimi man fetur inda ya yi yunƙurin cinnawa bankin wuta a Ogun.
Wasu gungun 'yan fashi da makami sun dira bankuna biyu a garin Otukpo da ke jihar Benuwai, sun bude wuta ta yadda kowa ne mai rai ya fara gudun neman tsira.
Yan Najeriya sun yi wa titunan Lagas tsinke don yin zanga-zanga kan yawan cajin da bankuna ke yi masu yayin da suka yi kokarin jan hankalin bankunan.
Kusan duk wani kamfani da aka rufewa akawun ya kubuta daga takunkumin CBN. Abin ya shafi kamfanonin Bamboo, Nairabet, abokiFX da assun Zahraddeen Haruna Shahru
Bankunan Najeriya na ƙara faɗaɗa harkokin kasuwancin su a nahiyar Afrika. Bankin Access yana a sahun gaba inda ya siya wasu bankuna biyar a nahiyar Afrika.
Mutane na cigaba da wahala, N500 da N1000 da CBN ya karbe sun gagara dawowa bankuna. ‘Yan kasuwa, masu sana’ar hannu, dalibai da masu POS su na kuka har yau.
Gidajen mai da sauran ƴan kasuwa da masu motocin haya sun ƙi cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin N500 da N1000 duk kuwa da umurnin da kotu ta bayar..
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya koka kan rashin sababbin kuɗaɗe a hannun mutane. Gwamnan ya bayyana cewa, har yau baya da sabbin kuɗin a hannun sa.
Guaranty Trust Bank - Gtbank
Samu kari