Labaran kasashen waje
Kashim Shettima ya tafi Brazil don wakiltar Tinubu a taron COP 30, inda zai gabatar da jawabi kan yanayi, makamashi, da kasuwar carbon domin ci gaban Najeriya.
Wasu jami'an sojoji sun shiga hannu bayan an zarge su da yunkurin gudanar da juyin mulki a kasar Guinea-Bissau. Hakan na zuwa ne ana shirin fara kamfen na zabe.
Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasar Tanzania. An sanar da sakamakon zaben ne a yau Asabar. Za a rantsar da Samia Suluhu Hassan yau Asabar.
Jagoran adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya zargi gwamnati da kulla shirin tsoratarwa da garkuwa da iyalansa bayan zaben shugaban ƙasa da aka yi.
Rundunar sojojin ruwa ta kasar Amurka ta tabbatar da hatsarin jiragenta biyu a tekun kudancin China, ta ce babu wanda ya rasa rayuwarsa a hadurran biyu.
Hukumomi sun sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Kamaru. Shugaba Paul Biya, ya doke abokin hamayyarsa, inda zai ci gaba da jan ragamar kasar.
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya shiga gidan yari bayan an kama shi da laifin karbar kudin kamfen daga Gaddafi, amma ya ce gaskiya za ta bayyana.
Fitaccen jarumin Bollywood, Asrani, ya rasu yana da shekara 84 bayan fama da matsalar numfashi. An fi saninsa da rawarsa ta “fursna” a fim din Sholay.
Isra’ila ta kai hare-haren sama a Gaza, ta kashe mutane 45 ciki har da mata da yara, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani.
Labaran kasashen waje
Samu kari