Babban kotun tarayya
Bayan shafe tsawon lokaci ana rigima kan kujerar sarauta, kotun daukaka kara a Ibadan ta yi zama kan rigimar sarauta a jihar Oyo kan kujerar Soun na Ogbomoso.
Dan majalisa, Hon. Philip Agbese ya karyata zargin da shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan ya yi masa ne neman a ba shi cin hanci da rashawa.
Mai martaba Ohinoyi na Ebiralanda ya koma kan karagar mulki da kotu ta ba da umarnin kowa ya tsaya a matsayinsa har sai kotun ɗaukaka kara ta yi hukuncin ƙarshe.
Kotuna su na taka rawa wajen sauke sarakuna masu daraja daga kan karagar mulki, Legit Hausa ta tattaro maku manyan sarakunan da shari'a ta sauke.
Bayan Kungiyar NBMOA ta maka Arewa24 a gaban kotu bisa zargin gudanar da ayyuka ba tare da lasisi ba a Najeriya za a saurari shari’ar a birnin Abuja.
Bayan zaman babbar kotun Abuja, fitacciyar yar gwagwarmayar nan, Naja'atu Mohammed da Salomon Dalung sun nuna ɓacin ransu kan kama Farfesa Usman Yusuf.
Shaidan jam'iyyar APC a kotun sauraron karar zaben Edo ya ce an yi tafka magudi a zaben. Ya ce an samu karin kuri'u sama da adadin wadanda suka yi rajista.
Yayin da ake tuhumar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta NHIS, Babbar kotun Abuja ta ki amincewa da ba da belin Farfesa Usman Yusuf kan badakalar kudi.
Kotun kolin Najeriya ta kawo ƙarshen taƙaddama kan sauya shekar ƴan Majisar dokokin Ribas 27, ta sallami ƙarar da Gwamna Fubara ya ɗaukaka zuwa gabanta.
Babban kotun tarayya
Samu kari