Nade-naden gwamnati
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bai wa Kwamishinonin jihar wa'adin kwanaki 10 da su rubuto dukkan ayyukan da suka aikata a ofisoshinsu.
Stella Okotete da Nasir El-Rufai suna cikin wadanda aka hana su zama Ministoci. Idan da akwai zancen tsaro, Okotete ta ce babu ta yadda za a bari ta zama Darekta.
Nnaemeka Obiareri, ya zargi gwamnati da batar da N23tr a iska. A lokacin Muhammadu Buhari yana mulki, ana zargin an karbi bashin N23tr a hannun bankin CBN.
Tsohon Gwamnan Zamfara ya zama gwarzon Ministoci. Kungiyar matasa ta ce a duk ministocin da Bola Ahmed Tinubu ya nada, babu mai kokari kamar Bello Matawalle.
An raba sama da Naira tiriliyan 6 daga asusun tarayya na FAAC a shekarar bara. Mun kawo bayanin kudin da aka ba kowane Gwamna daga FAAC a shekarar ta 2023.
Gwamna Nasir Idirs na jihar Kebbi ya sanar da rusa dukkan ciyamomin kananan hukumomi 21 a jihar inda ya yi alkawarin ba zai ya da su ba a harkokin gwamnatin jihar.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedayiwa, ya naɗa wasu mutum hudu a matsayin kwamishinoni mako biyu bayan ya tsige su daga mambobin majalisar zartaswa SEC.
Tsohon Akanta Janar a Najeriya, Ahmed Idris ya bayyana yadda hukumar EFCC ta yaudare shi kan amincewa da hannunsa a badakalar naira biliyan 109.4.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris Malagi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri akan sauye-sauyen gwamnatin Bola Tinubu, ya jaddada cewa akwai alkairi.
Nade-naden gwamnati
Samu kari