Nade-naden gwamnati
Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da cewa an dage shirin tantance sababbin Ministoci da shugaban ya nada da aka shirya yi a yau Talata 29 ga watan Oktoban 2024.
Majalisar dattawa ta fara shirin tantance mutum 7 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sababbin ministoci bayan ya yi garambawul.
Wani lauya ya tono kuskuren Bola Tinubu wajen nada ministoci da ya yi karo na biyu bayan korar wasu ministoci. Lauya ya ce Tinubu ya karya doka kan nada ministoci.
Tsohon ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya gana da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kawu Sumaila a gidansa.
A ranar Laraba Bola Tinubu ya tabbatar da korar ministoci 5 daga aiki tare da naɗa wasu sababbi, ya masu fatan alheri a duk lamurran da suka tasa a gaba.
Jigo kuma Tsohon dan takarar a Majalisar Tarayya a karkashin PDP a jihar Kogi, Austin Okai ya caccaki Bola Tinubu kan garambawul da ya yi a gwamnatinsa.
Shugaban cocin INRI, Primate Elijah Ayodele ya soki garambawul da Shugaba Tinubu ya yi a majalisar ministocin kasar nan, inda ya ce ba wadanda ya kamata aka kora ba.
Matan da za su zama ministoci a gwamnatin Bola Tinubu sun hada da Dr. Suwaiba Said Ahmad. Su ne sababbin matan da suka shiga gwamnatin APC mai mulki.
An kafa kwamiti da zai yi aiki a Majalisa ya yi bincike kan yadda aka dauki ayyuka a wasu hukumomi. Za a gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu.
Nade-naden gwamnati
Samu kari