Labaran Kwallo
An shiga jimami yayin da tsohon dan wasan kasar Jamus da Bayern Munich, Andreas Brehme ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 63 a kasar Jamus.
An yi ta yada wani faifan bidiyo mai nuna cewa mai tsaron gidan Ivory Coast ya yi amfani da laya a wasan karshe na AFCON 2023 tsakaninsu da Najeriya.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jadawalin ne a yau Alhamis 15 ga watan Faburairu wanda ya kunshi kasashen Afirka da sauran kasashen duniya.
Wani sojan Najeriya da ya samu rauni a fagen daga yayin kare martabar Najeriya, ya soki matakin Tinubu na ba 'yan wasan Super Eagles kyaututtuka masu gwabi.
Dan wasan tawagar Super Eagles, Sadiq Umar ya yi martani kan caccakar Alex Iwobi da ake yi a kafafen sadarwa inda ya ce shi ba Iwobi ba ne a yi hankali.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya baiwa daukacin ‘yan kungiyar Super Eagles lambar karramawa ta kasa ta 'Member of the Order of Niger (MON), da kyautar gidaje a Abuja.
Ahmed Musa, kyaftin tawagar Super Eagles ta Najeriya, ya yaba da juriya, jajircewa da sadaukarwar da 'yan wasan suka nuna a wasan karshen na AFCON 2023.
Mai horar da tawagar ƴan wasan Najeriya, Jose Peseiro, ya bayyana wasa yan wasan ƙasar Ivory Coast sun shammaci Super Eagles a wasan karshen da aka fafata.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Peter Obi, sun yaba da kokarin da 'yan wasan Super Eagles suka yi a wasan karshe na AFCON 2023.
Labaran Kwallo
Samu kari