Jihar Edo
Yayin da zaɓen jihar Edo ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta roki majalisar dokikin jihar ta gaggauta tsige Gwamna Obaseki kan kalaman da ya yi a bidiyo.
Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta bayyana fushinta kan komawar mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu zuwa jam'iyyar APC. Ta ce hakan ya nuna son kansa a fili.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin kwato jihar Edo daga hannun jam'iyyar PDP. Ya fara shirin cimma wannan kudirin.
Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya watsar da jam'iyyar PDP a jihar tare da komawa APC yayin da Abdullahi Ganduje ya karbe shi.
Shugaban APC na jihar Edo, Jarret Tenebe tare da wasu manyan ƙusoshi sun kai wa mataimakin gwamnan Edo Philip Shaibu ziyara har gida a Benin ranar Jumu'a.
Kwamared Philip Shaibu, wanda kotu ta mayar kan kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo ya zargi Gwamna Godwin Obaseki na shirya yadda za a kashe shi.
Miyagu sun kai mummunan hari kan dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo inda suka YI sanadin mutuwar dan sanda da ke tsaronsa.
Ga dukkan alamu rigimar siyasa a jihar Edo za ta dawo sabuwa yayin Philip Shaibu ya tsallake Gwamna Godwin Obaseki, ya naɗa ma kansa sababbin hadimai.
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu ya bayyana cewa shi ɗan APC ne amma abin da ya riƙe shi a PDP shi ne bai sanar da barinta a hukumance ba.
Jihar Edo
Samu kari