Daukan aiki
Gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano wasu likitoci da suka ajiye aiki amma har yanzu suna karbar albashi daga gwamnatin jihar. Za a dauki mataki akan su.
A cewar Dr. Ish Adagiri, hukumar asibitin kwararru a Kogi ta samu izinin daukar sabbin likitoci tun lokacin Yahaya Bello, amma har yanzu ba wanda ya nema
Wata ‘yar Najeriya ta ce naira 170,000 ne za ka biya kudin bizar zuwa Norway, kuma ta fada wa mutane yadda ake samun takardar. Mutum na iya zama dan kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka akwai sama da 'yan Najeriya 1,000 da aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya. An damfari kowanne akalla $10,000.
Kana bukatar aikin taimakawa da aikace-aikace a ofishin jakadancin Amurka da ke Lagas Najeriya. Duba albashin da za a biya da ranar rufe neman aikin.
Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin korar duk wani kwamishina da ya siyar da motar da gwamnatin ta ba shi. Akalla kwamishinoni 26 ne suka samu kyautar mota.
Dan Najeriya ya fadi wasu ayyuka guda biyu da mutum zai iya nema wanda ke biyan naira miliyan uku duk wata. Kamfanonin na aiki ne a Abuja kuma suna neman ma'aikata.
Akalla ma'aikatan gwamnatin tarayya dubu biyu ne ba za su samu albashin watan Nuwamba ba. Hakan ya faru sakamakon samun matsala da suka yi a tsarin IPPIS.
Ma'aikatan jinya su yi wa mara lafiya addu'a laifi ne a kasar Ingila. An ruwaito cewa 'yar Najeriyar ta yi wa wani mara lafiya addu'a ne, shi kuma ya yi kararta.
Daukan aiki
Samu kari