Kotun Kostamare
Jami'an 'yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ake zargin sun hallaka jami'in dan sanda a kauyen Konkiyel cikin karamar hukumar Darazo da ke jihar Bauchi.
Kotun da ke zamanta a jihar Ogun ta daure ya da kanwa, Gbenga da Funmilayo Elegbede kan zargin satar man goge baki bayan sun fasa shago da satar wasu kaya.
Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta daure wata mata kan zargin cizon mai musu sulhu yayin da su ke fada, Alkalin kotun ya bukaci ta biya Naira dubu 500 na beli.
Wata mata ta nemi wata kotu da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar Kwara da ta raba aurenta da mijinta saboda ya gaza sauke nauyinta da Allah ya ɗora masa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar da mace ta farko, Dije Audu Aboki a matsayin shugaban alkalan jihar, Abba ya nemi goyon bayanta a harkokin rusau
Babbar kotun da ke zamanta a Ilorin da ke jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa kan wani Mohammed Kazeem da zargin ya kashe makwabcinsa ana daf da daura aurensa.
Wata mata mai suna Hauwau Abubakar ta maka mahaifiyarta a kotu don ta nemo mata mahaifinta ganin yadda kannenta da suke zama wuri daya su ke mata gori a kullum.
Wata kotu da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar Kwara ta tura wata shugabar masu addinan gargajiya Iya Osun gidan yarin saboda cin mutuncin malamin addini.
Wani matashi ya tsere daga gidan kaso watanni hudu kafin wa'adinsa, an sake kama shi ya na aikata laifuka tare da yanke masa hukuncin shekaru 40 a gidan kaso.
Kotun Kostamare
Samu kari