Ayyuka mafi kyawu a Najeriya
Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya ragewa ma'aikata lokacin aiki domin su sami isasshen lokacin zuwa tafsir da yin wasu ibadun a watan Ramadan.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da shirin ciyar da mabukata a fadin jihar, inda ake sa ram mutum 91,000 ne za su samu buda-baki a kowacce rana.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana shirin da ta yi wa malaman jihar daga kan limamai, mataimakansu, ladanai da sauran kungiyoyin addini da watan Ramadan
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa al'umar da yake wakilta ne ke karfafa masa gwiwa wajen gudanar da manyan ayyukan ci gaban da ya dauki idon duniya.
Kamfanin raba wutar lantarki na Kaduna watau KAEDCO ya sallami ɗaruruwan ma'aikata daga aiki, zanga-zanga ta ɓarke a ofishin kamfanin da ke cikin Kaduna.
Kungiyar kwadago ta ƙasa reshen jihar Kano ta ba Abba Kabir Yusuf lambar yabon gwamnan da ya fi kishin ma'aikata saboda yadda yake inganta walwalarsu.
Hukumar EFCC ta ce duk wanda ya taka doka za ta taka shi, ta sanar da korar jami'anta 27 daga aiki bayan samunsu da laifin cin hanci da rashin ɗa'a.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya sallami dukkan ƴan majalisar gudanarwa na manyan makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar Edo nan take.
Majalisar wakilan kasar nan ta bijiro da kudirin da zai rika sa wa shugaban kasa linzami kan gudanar da gwamnati tare da tabbatar da ba da bayanan ayyuka.
Ayyuka mafi kyawu a Najeriya
Samu kari