Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar ya yi magana kan manufar kafa hadakar 'yan adawa. Ya ce ba don cika burin manyan jagororinta ba ne.
Jam'iyyar haɗaka watau ADC ta ce gwamnoni a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya sun amince za su haɗe da ƴan adawa domin ceto ƙasar nan a zaɓen 2027.
Wata lauya a Najeriya, Titilope Anifowoshe, ta yi magana kan hadaka inda ta shawarci ADC da ta fitar da dan takara mai gaskiya da kwarjini ga matasa.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedayiwa ya buƙaci gaba ɗaya ƴan adawar Najeriya su birne burinsu na neman takara, su goyi bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya ce jam'iyyar ADC za ta karɓi mulki daga hannun APC a 2027, yayin da manyan jiga-jigan PDP, APC da SDP suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar a Ekiti.
Jam'iyyar SDP ta ce ta sallami Nasir El-Rufa'i daga harkokinta har zuwa shekara 30 masu zuwa. SDP ta ce El-Rufa'i bai taba rajista da ita duk da ikirarin da yake yi.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne jagoran siyasar Arewa duk da cewa ya fita daga PDP zuwa ADC. Ya ce PDP za ta dawo da karfinta.
Jam'iyyar ADC reshen jihar Benue ta fito ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar ke daukar nauyinta. Ta ce ba gaskiya ba ne.
Jam'iyyar ADC ta masu hadaka ta yi magana kan dan takarar shugaban kasan da take goyon a zaben 2027. Ta bayyana cewa duk mai son yin takara tana tare da shi.
Atiku Abubakar
Samu kari