APC
Primate Ayodele a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, ya ce rigimar zaben gwamnan Filato na 2023 na da sarkakiya. Ayodele ya ce Gwamna Mutfwang na bukatar addu’a.
An bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kori mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, saboda kalaman da ya yi kan gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta fara fuskantar ƙalubale kan tsadar fom ɗin tsayawa takara a inuwarta gabanin babban zaɓen 2027.
An yi watsi da rade-radin cewa Gwamna Lawal Dauda na jihar Zamfara ne ya dauki nauyin tawagar lauyoyin Atiku Abubakar a shari’arsu da shugaban kasa Bola Tinubu.
Bayan sauraron kowane ɓangare, Kotun ɗaukaka kara mai zsma a Abuja ta jingine yanke hukunci kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin Kotun zabe, inda ta fatattaki kararrakin jam'iyyun PDP da LP da suka kalubalanci nasarar Gwamna Sanwo-Olu na jihar Lagas.
Bayan hukumar INEC ta tabbatar da wanda ya yi galaba a zaben Kogi, Ahmed Usman Ododo yayi bayanin yadda Shugaban kasa da Ganduje su ka taimakawa nasarar APC.
Yayin da ake ci gaba da shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto, kotun daukaka kara ta adana hukunci kan zaben da ake ci gaba da yi bayan hukuncin karamar kotu.
Gwamna Sule Abdullahi na jihar Nasarawa ya bayyana cewa akwai alamun sabbin fuskoki na shigo wa jihar yayin da ake shirye-shiryen yanke hukunci a gobe Laraba.
APC
Samu kari