Abun Bakin Ciki
An shiga jimami a jihar Enugu bayan rasuwar babban basaraken gargajiya, Mai Martaba, Igwe PD Uzochukwu, kwana guda kafin cikar sa shekara 90 a duniya.
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Hon. Maruf Musa, a ƙaramar hukumar Ogun Waterside.
Fusatattun mutane sun ƙona ofishin NSCDC a Dawakin Kudu, jihar Kano, tare da kashe mutane 3 da ake zargi da sata, yayin da jami'an tsaro 3 suka jikkata a hargitsin.
Wata uwargida ta kashe mijinta Momo Jimoh Jamiu a Kogi bayan ya kara aure, har ma matar ta haifa masa magaji. Rundunar 'yan sanda na farautar matar da ta tsere.
'Yan daba sun yi wa dan uwan tsohon gwamna tsirara, sun kuma lakada masa duka bisa zargin yana batanci ga mai martaba sarkin Benin. Godwin Obaseki ya yi martani.
An shiga tashin hankali a Sabuwar Unguwa da ke Katsina biyo bayan kisan wasu matasa biyu, ciki har da 'Kuda'. Matasa sun kona ofishin NSCDC da raunata 'yan sanda.
Jam’iyyar NNPP ta amince ‘ya’yan marigayi ‘yan majalisar Kano, Sa’ad Aminu Sa’ad da Nabil Aliyu Daneji, su fafata a neman kujerun da suka zama babu kowa.
Mutane 7 daga ƙauyen Lawanti a Gombe sun rasu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri yayin da suke kan hanyar zuwa biki, in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Wani matashi mai shekaru 19 a duniya da ke ƙungiyar mafarauta, ya rasu sakamakon fashewar bindiga bisa kuskure a unguwar Alkahira da ke Jihar Gombe.
Abun Bakin Ciki
Samu kari