Abun Bakin Ciki
Masana'antar shirya fina-fina ta Nollywood ta tafka babban rashin jarumi kuma furodusa mai suna Charles Owoyemi bayan ya sha fama da gajeruwar jinya.
An shiga jimami bayan sanar da rasuwar shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na kasa baki daya, Cif Emmanuel Iwuanyanwu a yau Alhamsi 25 ga watan Yulin 2024.
Allah ya karbi rayuwar shugaban cibiyar nazari da bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC), Farfesa Ismail Junaidu a yayin da ya ke halartar taron kwamitin tuntuba kan ilimi.
Rahotanni daga jihar Osun sun tabbatar da cewa an yi asarar rayuka biyu a rikicin da ya ɓarke kan sarauta a yankin ƙaramar hukumar Ayedaade ranar Talata.
An shiga jimami bayan mutuwar fitaccen basarake da ake kira Osi Balogun na Ibadanland, Oba Lateef Gbadamosi Adebimpe a jihar Oyo a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024.
Yanzu muke samun labarin rasuwar fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Suleiman Alaƙa. An ce jarumi Suleiman ya rasu ne a yau Litinin, 22 ga Yuli.
Hukumar SEMA a jihar SOkoto ta tabbatar da rasa gidaje 1,664 sakamakon mamakon ruwan sama da ya samar da ambaliyar ruwa a wasu garuruwan dake jihar.
Matashin da ya yi hudubar jefo malamai masu hana zanga-zanga daga minbari mai suna Junaidu Abdullahi ya gamu da matsala bayan jefa shi gidan yari.
Wani fusataccen Fasto a jihar Enugu mai suna Linus Okwu ya zane mambobin cocinsa saboda sun ki share harabar wurin ibadar yadda ya umarce su gaba daya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari