Abun Bakin Ciki
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya yi alhinin rasuwar tsohon sanatam jihar, Brambaifa, wanda Allah ya yi wa rasuwa a wani asibiti a birnin tarayya Abuja.
Iyalai sun tabbatar da cewa gawar sanatan Nasarawa ta Arewa, Godiya Akwashiki ta iso Najeriya, kuma ana ci gaba da shirye-shiryen yi masa sutura a Abuja.
An binne tsohon Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Lawal Kauru, a Zaria bayan ya rasu yana da shekaru 78 a asibitin koyarwa na ABUTH da ke Shika.
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan mutum 30 a kasuwar jihar Niger, tare da jajantawa jihar Yobe kan haɗarin jirgin ruwa da ya kashe mutane 25.
Gobara ta lalata ofisoshi da taskar makamai ta rundunar ‘yan sandan Mopol 13 a Makurdi, jihar Benue; rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da fara bincike.
Mutum 25 sun rasu, 14 sun ɓace a haɗarin jirgin ruwa a Nguru, Yobe; Hukumar SEMA ta ceto mutum 13 yayin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.
Cocin Katolika na Issele-Uku a Jihar Delta ya tabbatar da rasuwar Limami kuma Fasto Stephen Chukwuma, wanda ya rasu a daren sabuwar shekara yayin huduba.
Za a yi jana’izar abokan Anthony Joshua biyu da suka rasu bayan hatsarin mota a Najeriya, an shirya sallar a Masallacin London ranar Lahadi, 4 ga Janairu 2026.
Tsohuwar ministar kuɗi, Kemi Adeosun, ta ce manyan maƙiyanta a gwamnatin marigayi Buhari sun yi amfani da batun shaidar NYSC wajen tilasta mata murabus.
Abun Bakin Ciki
Samu kari